Hajj2025: YADDA AIKIN JIGILAR ALHAZAN JAHAR KATSINA YAYI NASARA - GM FAAN
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Kamar kowace shekara, a bana ma hukumar kula da filayen sabka da tashin jiragen sama ta ƙasa a jahar Katsina ta yaba da irin yadda aka gudanar da jigilar alhazan jahar tun daga farkon tashi har kammala aikin acikin nasara.
Babban Manajan hukumar a jahar Katsina Alhaji Usman Lawal Usman ya shaidawa wakilin mu haka a wata tattaunawa da suka yi da shi ta wayar salula a birnin Katsina. Alhaji Usman ya ce, "duk da cewa a bana jigilar alhazan ba kamar yadda aka yi na shekarun baya ba ne, domin a wannan shekara jirage huÉ—u ne aka samu da suka gudanar da aikin, hakan yasa mu kan mu ma'aikatan bamu samu wasu matsalolin azo a gani ba in ka É—ebe na ajizancin É—an-adam. Kuma da ma ka sani dui shekara kafin a fara jigilar maniyyatan muna zama tare da su jami'an hukumar jin daÉ—in alhazan na jahar domin tattaunawa tare da kawo tsare-tsaren domin ganin an tafiyar da aikin cikin nasara. Wannan zaman taron ana yin shi tare da sauran jami'ai masu ruwa da tsaki akan gudanar da aikin don ganin an haÉ—a hannu an cimma nasara".
Babban Manajan yace, duk da ɗan samun banbancin lokacin zuwan jirgi da aka samu, wannan bai hana gudanar da aikin kamar yadda aka tsara ba. "In ka lura, an samu zuwan jirgi har sau biyu a cikin kwana guda a lokacin dawowar alhazan bayan sabke farali. Sannan idan ka lura, a bana, mu a namu sashen, mun ƙara ɗaukar wasu matakan duk da cewa dama akwai su a duk inda filin jirgi yake, amma mu anan jahar saboda wani lokaci ne na tara mutane mabanbamta waɗanda ma wasun su sai dai su ji sunan filin jirgi amma basu taɓa zuwa ba, saboda haka muka ƙara tsaurara tsaro saboda halin da ake ciki don kada mu muna can muna wata hidimar a samu waɗanda zasu yi shigar burtu. Kaga ga jami'an tsaro nan iri-iri baya ga sojoji da muke haɗe da su. In ka tuna a bara ma mun ɗauki irin wannan mataki musamman akan masu zowa tarbar alhazai. To a bana har 'yan yin rakiya mun ɗauki matakin haɗin guiwa da ita hukumar jin daɗin alhazan".
Alhaji Lawal wanda ya jinjinawa dukkan abokan da suka gudanar da aikin Hajjin na 2025 har aka gama lafiya, ya kuma jinjinawa gwamnatin jahar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Umar Dikko Radda bisa ga irin goyon baya da kuma basu duk wani abin da suka nema daga gwamnatin don ganin an yi aikin cikin nasara. Sai dai ya ce, a matsayin ɗan-adam ajizi wanda baya rasa yin kuskure a wani wurin, ya ɗaukar matakin rage amfani da injin dake ba filin hasken wutar lantarki in babu ta ƙasa har sai lokacin da aka tabbatar da sabkar jigi, akwai yuwuwar bai yiwa wasu daɗi ba, amma saboda fahimtar dalilan yin hakan bai kuma kawo wani tsogumi ba. A ƙarshen Babban Manajan ya ƙara yin kira ga jama'a da su ci gaba da basu haɗin kai da kuma ƙara fahimtar yanayin aikin su ba wai sai a lokacin jigilar Alhazai ba, domin shi filin jirgin sama ya sha bamban da kowane irin wurin zuwan jama'a saboda dokoki da ƙa'idojin suna da yawa.