SAI JAMA'A SUN TAIMAKA ZA A YI NASARAR MAGANCE MATSALAR TSARO A KATSINA - Kwamishina tsaro
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar Katsina Dokta Nasir Ma'azu Ɗanmusa ya ce, sai jama'a sun bayar da hadin kai za'a iya shawo kan matsalar a faɗin jahar. Kwamishinan wanda ya baiyana haka a wani taron manema labarai da ya gabatar a sashen 'yan jaridu na gidan gwamnatin jahar ya ci gaba da cewa, "babbar matsalar da ake samu wadda har kullum take kawo cikas ga batun dakile matsalar tsaron ita ce ta masu ba ɓarayin dajin nan da ake kira Infoma labaran sirri da kuma yadda zasu shigo cikin gari su yi abin da suke so ba tare da fuskantar wata matsala. Daga cikin irin waɗannan mutane muna da labarin ɗan da bayar da bayanin yadda aka zo aka sace uban shi aka yi garkuwa da shi har sai da aka biya naira milyan talatin shi aka bashi milyan takwas aciki. Da kuma wanda yasa akayi garkuwa da uwa ko ƙanwa ko makwabtan su wanda duka-duka abin da ake basu ba abin da ya taka kara ya karya ba ne. Sun manta da cutarwar da suke yiwa kan su tun daga nan duniya kafin aje kiyama".
Kwamishina Ɗanmusa wanda yayi bayani mai tsawo akan wannan matsala ta tsaro da kuma irin ƙoƙarin da gwamnati ke yi don kawo ƙarshen abin, har ila yau, ya ƙara azawa jama'ar gari laifi na rashin ɗaukar matakin da ya dace tare da bayar da bayanan sirri ga duk wani wanda suke zargi da alaka da su 'yan bindigar domin daukar mataki. Ya ƙara da cewa, muddin jama'a basu kawar da tsoro ko shakku akan baiyana irin waɗannan infoma dake cikin su ba, to kullum ana tufka da warwara kenan. Kazalika, Dokta Nasir ya yaba da irin yadda matakan sulhun da wasu 'yan bindigar suka nema aka yi. Saidai ya ƙara jaddada matakin gwamnatin jahar na cewa ba zata nemi sulhu da masu aikata aiyukan ta'addanci ba sai fa in sune suka nema da kansu kuma bisa wasu sharuddan da za'a gindaya. Doktan ya ce, "gwamnati ta samu nasarori a wannan fanni na shawo kan matsalar tsaro a fadin jahar. Har'ila yau, ta bayar da tallafi ga wasu al'ummomin da wannan hari na 'yan bindiga ya rutsa da su. Saidai kuma ina ƙara kira ga jama'a da su zage damtse wajen bayar da kariya a tsakanin su ta waɗannan mutane, su kuma ci gaba da baiyana duk wani wanda suke zargin baiwa.'yanbidar bayanan sirri tare kuma da tona asirin duk wani wurin da suke zaton maboyar 'yan bindigar ne domin daukar mataki.
Kwamishinan tsaron ya ce, ba kamar yadda wasu ke tunani ba na cewar a rika kaiwa su wadannan 'yan bindigar hari da bamabamai inda yace, shi harin bam ba kamar na bindiga ba ne, sai ana da tabbacin inda za' a kai shi. Anan ne ya ƙara jaddada wancan kira ga jama'ar na bayar da sahihan bayanai ga jami'an tsaro don sanin irin matakin da zasu dauka.