Hajj2026: ƘASAR SAUDIYA TA FITO DA WASU DOKOKI GA MANIYATAN AIKIN HAJJIN 2026

Hajj2026: ƘASAR SAUDIYA TA FITO DA WASU DOKOKI GA MANIYATAN AIKIN HAJJIN 2026

Ƙasar Saudi Arebiya ta fito da wasu dokoki guda huɗu(4) ga maniyatan dake son zuwa aikin Hajjin shekarar 2026.
Dokokin da ƙasar ta fitar su ne, 1. Babu batun ƙarin lokacin da za'a biya kuɗin zuwa aikin da zarar wa'adin da aka baiyana ya cika. 2. Sai an tabbatar daga asibiti cewar maniyacin yana da ƙoshin lafiya. 3. Ba za'a bar masu ciwon ƙwada ko hanta da sauran cututtuka masu tsanani zuwa aikin ba. 4. An hana mata masu juna biyu da kuma masu taɓin hankali zuwa aikin Hajjin na 2026.
Ƙasar ta Saudiya ta jaddada ɗaukar matakin horo mai tsananin ga duk inda aka saɓa ko karya wannan doka
Har'ila yau, ƙasar ta Saudiya ta fito da waɗannan dokoki yayin da lokacin ƙarɓar kudaden ajiya na naira milyan 8 da rabi da hukumar dake kula da harkokin aikin Hajji ta kasa NAHCON ta baiyana zuwa 8 ga watan Oktoba na 2025 wanda ta umarci hukumomin alhazai na ƙasar da su karba daga maniyatan su ke ƙara matsow. 
Wannan mataki na ƙasar ta Saudiya ya ci karo da kiraye-kirayen da wasu jama'a suka yiwa hukumomin da abin ya shafa na neman ƙarin wa'adin yayin da a hannu guda ya ƙara ƙarfafa wasu kiraye-kirayen da aka yiwa gwamnatocin jihohin arewa na su rantawa hukumomin alhazan jihohin kudin da zasu sayi waɗannan kujeru kafin ƙurewar lokacin domin cike gurabun da aka basu, inda za'a biya gwamnatin a lokacin da maniyatan suka cigaba da biyan. 

Post a Comment

Previous Post Next Post