Hajj2026: AN BA GWAMNATOCIN AREWA SHAWARAR RANTAWA HUKUMOMIN JIN DADIN ALHAZAN SU KUƊI DOMIN SU MALLAKI KUJERUN AIKIN HAJJIN 2026 - Sarkin Alhazan Katsina
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Anyi kira ga maniyatan jahar Katsina masu son zuwa aikin Hajjin 2026 da su yi hanzarin biyan kuɗin ajiyar su na naira milyan 8 da dubu ɗari 5 kafin ranar da hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta aiyana a matsayin ranar ƙarshe ta biyan, wato, 8 ga watan Oktoba na 2025.
Sarkin Alhazan Katsina wanda kuma shi ne Shugaban hukumar jin daɗin hukumar alhazai ta jahar Katsina Alhaji Kabir Bature sarkin Alhazai yayi wannan kira yayin hirar shi da wakilin mu ta wayar salula akan shirye-shiryen hukumar don tunkarar aiyukan Hajjin mai zuwa. Shugaban yace, tuni hukumar shi ta ci gaba da shirye-shiryen tun daga hedkwatar hukumar har zuwa ga sauran yankunan hukumar dake fadin jahar, musamman ta faɗakarwa tare da nuna muhimmancin biyan kuɗin ajiyar kafin ƙarewar wa'adin da aka bayar.
"An warewa jihar Katsina kujeru sama da dubu 3 daga NAHCON akan wannan aikin Hajji na 2026 wanda muke ta ƙoƙarin ganin an cika adadin waɗannan kujeru duk da cewa, lokacin da aka ɗiba domin biyan waɗannan kuɗaɗe yayi kaɗan ga kuma batun matsalar tattalin arziki da ake fama da ita".
"Duba da yanayin da kuma ƙurewar lokacin yasa nike bayar da shawara musamman ga gwamnatocin mu da cewa, muddin ana son Najeriya ta je aikin Hajjin na 2026 to lallai sai sun shigo domin baiwa hukumomin jin dadin Alhazan su rancen kudi domin sayen waɗannan kujeru da aka warewa jihohin su kafin lokacin ya ƙure. Suna iya sayen kujerun a matsayin rance ga maniyatan wanda zasu cire kuɗaɗen su a lokacin da maniyatan suka ci gaba da biya. Misali, ka ɗauki jaha ta Katsina, mafi yawan masu zuwa aikin Hajjin nan manoma ne, to kuma ga irin yadda daminar ta bana ta zo a wasu sassan, sannan kuma yanzu ne kayan amfanin gonar suke nuna wanda sai nan da ɗan wani lokaci za'a fara fitar da su, to kuma ance a biya kuɗin kafin ranar 8 ga watan Oktoba, kenan akwai yuwuwar inba gwamnati ta shigo wajen sayen kujerun ba, zaiyi wuya ace an samu mutun ɗari uku ba wai dubu 3 ba waɗanda zasu samu damar zuwa wannan aikin ibada. Saboda haka, ina kira da babbar murya da kuma bayar da shawara ga gwamnatin jihohi ba wai ta Katsina kawai ba, da su fito domin tallafawa wannan aiki ta hanyar bayan da wancan rance don sayen waɗannan kujeru ga maniyatan domin samun damar yawan waɗanda zasu sabke wannan farali tare da yiwa jihohin da ƙasa addu'a".
Idan za'a tuna, a can baya Gwamnan Jahar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya sha alwashin jagorancin sauran gwamnoni zuwa fadar gwamnatin ƙasa domin tattaunawa akan batutuwan da suka shafi aiyukan Hajjin a wata ganawa da suka yi da shugaban hukumar kula da Aikin Hajji ta kasa NAHCON a Abuja bayan kammala aikin Hajjin 2025.