Hajj2026: ANYI KIRA GA HUKUMAR NAHCON DA TA SAUDI ARABIA DA SU ƘARA WA'ADIN BIYAN KUƊIN AJIYA NA MANIYATAN 2026 - Maniyata

Hajj2026: ANYI KIRA GA HUKUMAR NAHCON DA TA SAUDI ARABIA DA SU ƘARA WA'ADIN BIYAN KUƊIN AJIYA NA MANIYATAN 2026 - Maniyata

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Duk da cewa gwamnatin jahar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda ta amincewa da cigaba da karbar kudin ajiyar aikin Hajjin 2026 na naira milyan 8.5 har zuwa 8 ga watan Oktoba, 2025, wanda hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Katsina ƙarƙashin jagorancin Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama ke ta ƙara tunasar da maniyatan jahar cewa, su ci gaba da biyan waɗannan kuɗi kafin ranar ƙarshe ta wa'adin da aka ambata domin samun damar cike gurbin kujerun da aka warewa jahar na sama da dubu uku, a inda jami'an hukumar dake yankunan ƙananan hukumomin jahar da suka hada da Daura, Dutsinma,Mani, Katsina, Kankiya, Malumfashi da Funtuwa ke cigaba da karɓar kudaden, kamar yadda aka san jahar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin dake sabke wannan nauyi tare da bin duk wata doka da oda.
Sai dai wakilin mu ya tuntuɓi wasu daga cikin maniyatan dake son sabke wannan nauyi da kuma waɗanda suka daɗe suna zuwa wannan aiki domin jin ra'ayoyin su akan wannan wa'adi. Alhaji Aminu na daga cikin waɗanda suka tuna baya da kuma lura da yanayin da ake ciki na yanzu. "Ni kai na lokacin da naje aikin hajji na har sau biyu, na biyun harma sai da aka fara jigila zuwa Makka na biya kudin kujerar, kuma ina jin a jirgi na uku na tafi. Amma yanzu irin wannan tashi na kama ka da hukumomin ke yi sai muga kamar ana son kodai a rage yawan masu zuwan ko kuma a hana baki ɗaya". Alhaji Aminu ya ƙara da cewa, idan har hukumomin Saudiya zasu yi la'akari da irin yadda wasu ƙasashen ke biyan kudin kujerun su, yana da kyau su yi la'akari da bambanci yanayi da wuri da kuma tattalin arziƙin wasu ƙasashen.
"Ka ga mu anan Najeriya yankunan arewacin ƙasar aka fi zuwa wannan aikin ibada. To kuma daga ciki yawan masu zuwan zaka ga manoma ne waɗanda sai sun yasar da amfanin gonar da suka noma suke samun kuɗin. To yana da kyau ita hukumar dake kula da harkokin aikin Hajjin NAHCON ta nusar da ita ƙasar ta Saudiya domin lura da wannan, ba wai kawai idan ance kaza su tsaya akan haka saboda tsari ne na Saudiyar. Yanzu ace, an bayar da sanarwar ajiyar kudi sama da naira milyan 8 acikin abin da bai wuce wata guda ba, ai mutun ko sata yake yi ba zai ajiye su ba balle ga mai kasuwa ko manomi".
Malama Rabi'atu, wata dattijuwa tace, shekaru biyu ajere take son zuwa wannan aikin ibada amma bata samu kudin da ake nema ba. "To gashi bana ina sa ran zuwa amma lokacin da aka ce a biya kudin yayi mani kadan. Yaron da zai cika mani kudin har yanzu bai fara fitar da kayan amfanin gonar shi ba, ga kuma yadda damanar ta zo. Kasan mu anan kudu noman shine babban abin alfaharin mu.
Kusan dukkan mutanen da aka tuntuba abu guda suke magana akai, wato, ƙara wa'adin da aka ɗiba wajen biyan kudin inba ana so a samu ƙaranci ko rashin zuwan baki ɗaya daga wasu sassan ba. Wasu kuma sun bayar da shawarar shigowar gwamnati domin ɗaukar matakin gaugawa akan abinda ya dace. 

Post a Comment

Previous Post Next Post