GOBE ALHAMIS MAHAJJATAN JIHAR KATSINA ZASU YI HAWAN ARFA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Alhazan jihar Katsina sun isa garin Munna domin haduwa da sauran musulmin duniya don gudanar da aikin hajjin bana. Mataimakin gwamnan kuma Amirul Hajjin jahar Katsina na shekarar 2025, Malam Faruk Lawal Jobe, Kakakin majalisar dokokin jihar tare da Babban Jojin Jahar mai shari'a Musa Danladi Abubakar da sauran Alhazai sama da 2000 daga jihar Katsina ne ke halartar aikin ibada na bana.
Alhazan da suka nuna jin dadinsu da shirye-shiryen da aka yi a garin Munna saboda zaman jiran gobe Alhamis don yin Arfa, sun yi fatan aikin hajjin bana zai samu gagarumar nasara.
Amirul Hajjin ya yaba da yadda mahajjata ke gudanar da ayyukan Hajji a kasa mai tsarki tare da umartar su da su ci gaba da yi wa jihar Katsina da Nijeriya addu’ar zaman lafiya da ci gaba a tsawon lokacin gudanar da ibada. Babban Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama ya bayar da tabbacin cewa an yi dukkan shirye-shirye domin jin dadin Alhazan jihar yayin da suke gudanar da ayyukan ibada.
A gobe Alhamis da safe ne mahajjatan zasu tashi zuwa Arafat domin gudanar da aiyukan ibada da suka hada salloli da addu'o'i da sauran ayyukan ibadar da ake gudanarwa a wannan rana.