Ranar Arfat: SAƘON TAYA MURNAR ARFA GA ALHAZAN JAHAR KATSINA

RanarArfat: SAƘON TAYA MURNAR ARFA GA ALHAZAN JAHAR KATSINA 

A yau Alhamis 5 ga watan Yuni 2025 wanda yayi daidai da 9 ga watan Zulhajj 1446 bayan hijirar Manzon tsira Annabi Muhammadu (SAW) daga Makka zuwa Madina, ita ce ranar da Alhazan jihar Katsina tare da na sauran duniya suka yi hawan Arfa wanda yake jigo a aikin Hajji.
Akan haka, a madadin kamfanin AK S-KUKA GLOBAL COMMUNICATIONS wanda aka fi sani da ASKGLOC NEWS, muna taya alhazan jihar murnar sabke wannan farali tare da sauran alhazan duniya baki. Allah ya karbi ibada da addu'o'in da aka yi da kuma waɗanda za'a ci gaba da yi.
Har'ila yau, kamfanin na taya Maigirma Gwamna Malam Dikko Umar Radda murna akan yadda alhazan jihar suka gudanar da wannan aiki na ibada ba tare da samun wata matsala ba tun daga gida har zuwa ƙasa mai tsarki. Kazalika, muna taya shi Maigirma Mataimakin Gwamna Malam Faruk Lawal Joɓe wanda kuma shi ne Amirul Hajj na wannan shekara tare da 'yan tawagar shi da su jami'an hukumar jin daɗin alhazan na jahar Katsina ƙarƙashin jagorancin Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama da kuma sashen gudanarwa na hukumar ƙarƙashin shugabancin hukumar Alhaji Kabir Bature sarkin Alhazai. Allah yasa yadda aka yi wannan aiki lafiya a gama shi lafiya, ya kuma maido da alhazan jihar gida lafiya tare da na sauran duniya.
Saƙo daga shugaban kamfanin
Kabir Ahmed S/Kuka 

Post a Comment

Previous Post Next Post