TAUSAYAWA MAJJATA NE YASA GWAMNA BIYA MASU KUDIN HADAYA - Zulaihatu Radda

TAUSAYAWA MAJJATA NE YASA GWAMNA BIYA MASU KUDIN HADAYA - Zulaihatu Radda
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
Uwargidan Gwamnan Jahar Katsina Malam Dikko Umar Radda Hajiya Zulaihatu Dikko Radda tace, tausayi tare da neman mahajjatan jahar su gudanar da aikin Hajjin su cikin kwanciyar hankali tare da samun na guzuri daga cikin kudaden da aka basu yasa Gwamna biya masu kudin hadaya na Riyal 600 kudin Saudiya.
Uwargidan ta baiyana haka a ranar Alhamis 22/5/2025 a filin jirgin sabka da tashi na Umaru Musa dake Katsina a bisa hanyar ta ta zuwa aikin hajji. Hajiya Zulaihatu wadda ta nuna gamsuwa akan irin yadda aikin jigilar alhazan ke gudana a yayin da jirgi na biyu na kamfanin Max Air ke yi, tace, gwamnatin Dikko kullum tunanin ta shi ne, yaya zata taimakawa al'umma da kuma hanyoyin cigaban jahar. Ta ƙara da jinjinawa su jami'an hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Katsina ƙarƙashin jagorancin Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama da sauran masu da tsaki na wannan aiki bisa ga irin yadda suka jajirce wajen ganin sun sabke nauyin da ya rataya kansu.
A nashi jawabin, Shugaban hukumar jin dadin Alhazan na jahar, Sarkin Alhazai Alhaji Kabir Bature cewa, "Allah zamu ci gaba da yiwa godiya bisa ga irin yadda ya bamu nasara akan aiwatar da wannan aiki tun daga farko har zuwa yau da jirgi na biyu ya tashi duk kuwa da É—an canjin lokacin tashin da muka samu. Wanna kuma ba komi bane idan aka yi la'akari da yadda aikin hajji yake".
Sarkin Alhazan wanda ya jinjinawa Gwamna Radda akan irin yadda yake ba wannan aikin ibada muhimmanci tare da basu kulawa akan duk wani abinda suka nema. Kazalika, Shugaban hukumar ya yaba da irin yadda maniyatan jahar suke bayar tun daga lokacin yi masu bita har zuwa tashin su. Ya Æ™ara da cewa, ba wai acikin jirgi ba, hatta da motoci da gidajen da aka sabkar da maniyatan akwai jami'an hukumar, masu wa'azi da duk wani jami'in da zai gudanar da wani aiki daga cikin hidimomin wannan aiki. Sarkin Alhazan ya Æ™ara jan hankalin maniyatan da su kiyaye dokokin wannan aiki da kuma Æ™asar ta Saudiya musamman a wannan lokacin da Æ™asar ta sake kawo wasu sabbin dokoki. Jirgin na biyu, ya tashi da maniyata 554 zuwa Æ™asar don sabke farali. 

Post a Comment

Previous Post Next Post