GIDAUNIYAR MANGAL TA KASHE NAIRA MILYAN 80 DON ƊAUKAR NAUYIN TIYATAR MASU YOYON FITSARI A KATSINA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Gidauniyar taimakon al'umma ta shahararren ɗan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Mangal dake Katsina, ta kashe sama da Naira miliyan 80 domin daukar nauyin yi wa marasa lafiyar yoyon fitsari aikin tiyata da kuma kula da su a jihar. Wani ɗan kwamitin amintattu na gidauniyar Mangal, Mista Husaaini Kabir, ya bayyana haka a Katsina ranar Asabar, a wajen kaddamar da atisayen na wannan lokacin.
Kabir ya ce tun daga lokacin da aka fara aikin marasa lafiya a kalla 3,000 ne suka amfana da aikin gudunmuwar daga cikin aiyukan guda 10 da aka gudanar a baya. Ya bayyana cewa a wannan kwata na biyu na shekarar, an ware sama da Naira miliyan 20 domin daukar nauyin aikin tiyatar yoyon fitsari ga majinyata sama da 100.
Wakilin kwamitin amintattu ya kara da cewa majinyatan da ba sa bukatar tiyata, za a duba su tare da basu magunguna kyauta. Kabir ya yi nuni da cewa, wannan karimcin wanda wani bangare ne na nauyin da ya rataya a wuyansu na zamantakewar al’umma, da nufin mayar da hankali ga al’umma, musamman ma marasa galihu.
A cewarsa, jama’a daga kauyuka daban-daban na jihar da jihohi makwabta da ma daga jamhuriyar Nijar, su ma suna cin gajiyar wannan aikin. Kabir ya ce babban burinsu shi ne su rage wa marasa galihu nauyi a kan harkokin kiwon lafiya, saboda da yawa daga cikinsu suna kokawa wajen biyan bukatun yau da kullum.
Ya bayyana cewa ana gudanar da aikin tantance mutanen ne a asibitin Amadi Rimi da ke karamar hukumar Batagarawa a jihar. "Gidauniyar ta hada ƙwararrun likitocin kiwon lafiya da kuma samar da magunguna masu inganci da kayan aikin likita don aikin tiyata," in ji shi.
Kabir ya kara da cewa gidauniyar ta musamman ce don karfafawa, ci gaba, ilimi, ayyukan jin kai da tallafawa marasa galihu ta fannin kiwon lafiya da fasahar tattalin arziki. Ya kuma bayyana cewa gidauniyar wadda aka kafa a shekarar 2016, ta kuma dauki nauyin aikin tiyatar ido, gwaiwa da sauran irin su ga dubban marasa lafiya.
Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, ma’aikacin kwalejin fasaha ta jiha, Malam Adamu Aliyu, ya yabawa wanda ya dauki nauyin wannan tallafin, inda ya ce ya dade yana neman irin wannan dama. A cewarsa, dan albashin da yake karba ba zai iya ba shi damar yin tiyatar ba, saboda kudaden sun yi yawa, yana mai rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya saka wa wanda ya dauki nauyin wannan aiki. Sauran wadanda suka ci gajiyar shirin sun kuma yaba wa wannan karimcin, sannan sun yi kira ga gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu, da sauran masu hannu da shuni da su yi koyi da irin aikin jin kai da tallafawa marassa karfi.