ƊAN MAJALISAR WAKILLAI YA GINA RIJIYAR BURTSATSE 71 A MUSAWA DA MATAZU
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Ɗanmajalisar wakillai na tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Musawa da Matazu daga jahar Katsina wanda kuma shi ne Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin cikin gida, Dujiman Katsina Honarabil Abdullahi Aliyu Ahmed ya gina rijiyoyin burtsatse 71 masu amfani da hasken rana a cikin al’ummomin dake fadin mazabarsa na tarayya wato, Musawa da Matazu domin samar da ruwan sha ga mazaɓun.
Kamar yadda wata sanarwar da Mataimaki na musamman akan harkokin yaɗa labarai ga Ɗanmajalisar Sardauna Francis ya sanyawa hannu yace, daga cikin wadannan rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana an gina uku (3) a kowace unguwa acikin unguwanni 11 na siyasa na karamar hukumar Musawa, yayin da aka gina hudu (4) a hedkwatar karamar hukumar ta Musawa wanda adadin rijiyoyin burtsatse ya kai 37 a Musawa kadai.
Honarabil Abdullahi Aliyu Ahmed ya kuma haka rijiyoyin burtsatse guda uku (3) masu amfani da hasken rana a kowace unguwa acikin unguwanni 10 na karamar hukumar Matazu da kuma wasu hudu (4) a hedikwatar karamar hukumar ta Matazu wanda ya kawo adadin sabbin rijiyoyin burtsatse a mazabar zuwa 71.
Kafin aikin hakar rijiyoyin burtsatse 71, dan majalisar ya dauki kwararrun masana muhalli wadanda suka gudanar da bincike kan yanayin kasa da yanayin ruwa domin tantance zurfin da kowane rijiyar burtsatse ke bukata da kuma hanyoyin hakowar da za su fi dacewa a kowace al’umma da za su amfana.
Kazalika, kowace daga cikin rijiyoyin burtsatse 71 da ke amfani da hasken ranan sai da aka yi gwajin karfin aiki tare da gwajin ingancin ruwan don tantance dacewarsa don amfanin dan Adam.
Har'ila yau, an ajiye na’urorin masu aiki da hasken rana don yin amfani da famfunan rijiyoyin burtsatse na kowace rijiyar burtsatse, ta yadda za su kara dawwama da dorewar aikin. Domin kare rijiyoyin burtsatsen daga masu kutsawa, an sanya shinge tare da kullewa, sannan al’ummar yankin sun zabi kwamitocin da za su inganta aikin da kiyaye wuraren da kuma tsara yadda ake amfani da rijiyoyin tare da hadin gwiwar kwararrun masana ruwa da gwamnati ta horar.
Aikin haƙar wadannan rijiyoyin burtsatse na da nufin samar da ingantaccen ruwa mai dorewa ga mazauna mazabar Musawa da Matazu tare da magance matsalar karancin ruwa tare da inganta tsarin kula da ruwa don bukatun gida da na noma.
Haka kuma ya kara jaddada kudirin Dujiman Katsina na farko na samar da ababen more rayuwa mai dorewa da kuma matsayar da ta dace kan ayyukan da ba su da inganci. Hakan dai na nuni da yadda ya jajirce wajen ganin ya magance bullar cututtukan da ake samu daga ruwa a mazabar.
“Wadannan rijiyoyin burtsatse guda 71 da ke amfani da hasken rana ba batun samar da ruwa ba ne kawai, sun shafi canza rayuwa ne domin samun ruwa mai tsafta yana da muhimmanci ga lafiya, ci gaban tattalin arziki da ci gaban al’umma.
“Da wadannan ayyuka, na tabbatar da cewa ‘yan yankin Musawa da Matazu da sauran al’ummomi da kauyukan da ke kewaye da su ba sa fama da karancin ruwan sha,” in ji dan majalisar tarayya.
Yayin da yake lura da cewa hakkin mazauna yankin ne su mallaki ayyukan ruwan, Honarabil Abdullahi Aliyu Ahmed ya bukace su da kada su bari a lalata rijiyoyin burtsatse.