JIRGIN FARKO DAUKE DA MANIYATAN JAHAR KATSINA YA TASHI ZUWA SAUDIYA

JIRGIN FARKO DAUKE DA MANIYATAN JAHAR KATSINA YA TASHI ZUWA SAUDIYA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
A da ƙarfe ɗayan daren lahadin nan jirgin farko ɗauke da maniyatan jahar Katsina 542 ya tashi zuwa Jidda a bisa hanyar su ta zuwa aikin Hajjin 2025. Maniyatan da suka fito daga ƙananan hukumomin Bakori Danja, Kankara da Faskari da wani Malunfashi gami da wani sashe na yankin Funtuwa, jirgin Kamfanin Max Air mai suna 5N HMM shi ne ya dauke su.
Lokacin da yake bankwana da maniyatan, Amirul Hajji kuma Mataimakin Gwamnan Malam Faruk Lawal Jobe wanda ya samu rakiyar Kakakin majalisar dokokin jihar Rt. Hon. Nasiru, shugaban hukumar jindadin alhazan Sarkin Alhazai Alhaji Kabir da Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Dankama tare da wasu daga cikin kwamitin shi Amirul kamar su Mai Shari'a Aminu Tukur Ƙofar Bai da wasu masu ruwa da tsaki akan wannan aiki na bana, suka rufa ma shi baya, ya yaba da yadda aikin wannan jigilar alhazai ta yau ta kasance. Amirul wanda ya nuna jin dadi da gamsuwa yace, lallai shirye-shiryen da suka domin ganin an aiwatar da wannan aikin Hajji na bana tun yanzu ya fara haifar da É—a mai ido ganin yadda maniyatan suka yi amfani da irin abubuwan da aka gaya masu a wajen taron bitar da aka yi kafin fara kwasar su zuwa Æ™asa mai tsarki. 
Tun farko, sai da shugaban ma'aitakatan gidan gwamnatin jahar Honarabil Abdulkadir Nasir ya jinjinawa Gwamna Radda musamman akan irin yadda ya Æ™ara daukewa maniyatan jahar É—aya daga cikin manyan wannan aiki na Hajji, wato, Hadaya ga maniya a Æ™alla 2047. Shugaban ma'aikatan yace, wannan Æ™uduri da kuma niya ta Gwamna Radda ba Æ™aramin abin alfahari ba ne duba da irin yadda kowace fuska yana Æ™oÆ™arin bayar da ta shi gudunmuwar. A bara ma sai da Gwamnan ya biyawa maniyatan kudin hadayar. 

Post a Comment

Previous Post Next Post