SAI MAI BIZAR AIKIN HAJJIN 2025 ZAI IYA SHIGA MAKKA

SAI MAI BIZAR AIKIN HAJJIN 2025 ZAI IYA SHIGA MAKKA.
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 


Hukumomin Saudiya sun kawo wani sabon tsarin binciken masu zuwa aikin Hajjin wannan shekara domin tabbatar da cewa waÉ—anda ke da Bizar aikin Hajjin 2025 ne kaÉ—ai zasu shiga birnin Makka domin gudanar da wannan aikin. 
Hukumomin sun baza jami'an tsaro a duk wata hanya ko saÆ™o wanda zai kawo mutun cikin garin na Makka domin tabbatar da cewa masu wannan biza ne kadai zasu shiga. Kamar yadda hukumomin suka sanar, sun É—auki wannan mataki ne domin yin awon gaba da É“ata gari da masu yin amfani da irin wannan lokacin domin shigowa garin na Makka. 
Wani maniyaci ya shaida mana cewa, daga Madina zuwa garin na Makka bai iya cewa ga yawan shingen binciken da ya gani domin tabbatar da sun kama duk wanda ya karya wannan doka. "Mun fi awa biyu a tsaye wajen binciken bamu tafi. Ana bin mutane É—aya bayan É—aya ana tambayar su. Duk wanda bashi da wata shaidar zuwa aikin ba to ya shiga cikin matsala".
Ƙasar ta Saudiya tace daukar wannan matakin ya zama wajibi domin wasu na amfani da bizar shigowa Æ™asar amma sai su wuce suyi aikin bayan bizar ta aikin Hajji daban take. 
WaÉ—anda ke cikin garin na Makka masu son zuwa Harami sai da Æ™waƙƙwarar shaidar zuwan domin nan ma akwai binciken Æ™waÆ™waf. Akan haka ake shawarar ta maniyyatan wannan aiki da su tabbatar da cewa suna tare da wata shaidar zuwa aikin na Hajji musamman katin shaida da hukumomin Alhazai ke bayarwa. 

Post a Comment

Previous Post Next Post