Kurfi: MATATTU NA DA HAƘƘI AKAN MU - Hon. Babangida
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Shugaban ƙaramar hukumar Kurfi Honarabil Babangida Abdullahi ya baiyana cewa, matattu ma nada haƙƙi akan su wanda ya kamata su sabke ballanta na ga masu rai. Shugaban ya baiyana haka ne a lokacin da yake ƙaddamar da gudunmuwar yadin likkafani bandir 60 da tukanen rufin kabari 1000 a duk mazaɓun ƙaramar hukumar 10. Honarabil Babangida ya ce, bayar da wannan gudunmuwa zai kawo sauƙin neman waɗannan kayan bukatuwa a duk lokacin da aka ce an rasa wani.
"Wasu lokuttan sai a taras kafin a samu waɗannan kaya a lokacin da aka rasa abin yana ɗaukar lokaci bayan kuma ance a gaggauta kai mamaci makwanci kada a tsawaita lokaci sai fa inda wata lalura. Sannan idan muka duba, wata rana mune za'a nemarwa waɗannan kaya ne".
Shugaban ya ja hankalin al'umma da su riƙa kulawa da maƙabartu saboda nan ne gidajen ƙarshe da mutun zai zauna aciki. "Ganin irin yadda addinin musulunci ya ba matacce da makwancin shi hakan yasa muma a ƙaramar hukumar mu zamu cigaba da bayar da irin wannan muhimmanci ba sai gare mu masu rai ba", inji Shugaban ƙaramar hukumar ta Kurfi Honarabil Babangida Abdullahi.
Wannan gudunmuwar ga waɗanda basu da rai da ita ƙaramar hukumar ta Kurfi tayi, gwamnatin Jahar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda tayi wani abu makamancin haka ƙarƙashin hukumar Zakka da Waƙafi. Gwamnatin a halin yanzu tana ci gaba da gyaran maƙabartar Ɗanmarna dake cikin garin Katsina wanda harda wajen ajiye gawa da fitar da hanyoyi da sanya lantarkai da sauran irin su. Manufar gwamnatin shine kiyaye shiga hakkin waɗannan bayin Allah dake kwance aciki.
Baya ga bayar da gudunmuwar likkafin da tukane, Shugaban ƙaramar hukumar Kurfi Honarabil Babangida Abdullahi ya kuma bayar da gudunmuwar kayan haihuwa ga mata masu juna biyu da ke zowa asibiti domim haihuwar. Shugaban anan ma yace sun lura da irin wasu matsalolin da masu haihuwar ke fuskanta ta wannan fuska. Kan haka yasa ya sayi kayan haihuwar kyauta ga duk wadda Allah yasa take da rabon amfana da su. Ya ƙara da cewaire-iren waɗannan kayan jinƙan daga wasu ɓangarorin suma anan nan ana shirya yadda za'a fito da su domin amfanan jama'ar ƙaramar hukumar.