ƘUNGIYAR POLO TA KATSINA TA JAJANTA TARE DA ADDU'AR SAMUN LAFIYA GA GWAMNA RADDA.
Kungiyar wasan Polo ta Katsina ta yi matukar jimami tare da alhinin jin labarin afkuwar wani karamin hatsarin mota da ya afku a yammacin ranar Lahadi 20 ga watan Yuli, 2025, wanda ya hada da mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, a kan hanyar Daura zuwa Katsina.
Kamar yadda shugaban ƙungiyar Alhaji (Dr.) Muhammadu Usman Sarki ya ce, "Alhamdulillah, muna godiya ga Allah madaukakin sarki da ya kare shi, kasancewar gwamnan bai samu wani mummunan rauni ba kuma yana cikin ci gaba da samun sauki tare da walwala".
Shugaban ya ƙara da cewa, suna tare da al’ummar jahar Katsina tare da ‘yan Nijeriya a ko’ina suke a wajen yiwa Gwamna addu’ar Allah Ya ci gaba da yi masa jagora, ya kuma kara mashi karfin guiwa da kuzari. Shugaba Alhaji Muhammadu yace suna yiwa sauran wadanda hadari ya rutsa da su. "Allah ya yi masa jagora, ya kuma kare shi, ya ci gaba da jajircewarsa wajen ganin jihar Katsina ta samu ci gaba", inji shugaban ƙungiyar.