SHUGABAN QASA TINUBU YA KAFA KWAMITIN JANA'IZAR TSOHON SHUGABAN QASA MUHAMMADU BUHARI DA ZA A YI A KATSINA.
Daga Kabir Ahmed S/Kuka.
Shugaban qasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da kundin tsarin mulki na kwamitin ministoci na jana’izar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR.
Kwamitin wanda sakataren gwamnatin tarayya, Sen. George Akume, CON ke jagoranta, yana da alhakin tsarawa da kuma gudanar da jana'izar marigayin dattijon a jihar ta Katsina. A cewar sanarwar da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a Mista Segun Imohiosen ya sanya wa hannu, sauran mambobin kwamitin sun haxa da - Mai girma ministan kuxi kuma ministan tattalin arziqi, Ministan kasafin kuxi da tsare-tsare, Ministan Tsaro, Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a na qasa.
Sauran sun haxa da Ministan ayyuka, Ministan harkokin cikin gida da Ministan birnin tarayya Abuja FCT. Ministan gidaje da raya birane Qaramin Ministan Lafiya da Jin Daxin Jama'a, Ministan fasaha, al'adu da tattalin arziqi. Mai baiwa shugaban qasa Shawara Kan Tsaro
Mashawarci na musamman ga shugaban qasa kan manufofi da daidaitawa. Babban mataimaki na musamman ga shugaban qasa kan harkokin siyasa da sauran su. Sufeto Janar na 'yan sanda, Darakta-Janar, Sashen Sabis na Jiha (DSS), Babban Hafsan Tsaro
Ofishin Babban Sakatare zai zama Sakataren Sakatariyar Kwamitin.
A wajen karrama marigayi shugaban qasa Muhammadu Buhari, shugaba Tinubu ya kuma umurci ma’aikatu da hukumomi da su buxe rajistar ta’aziyya a qofar ofisoshinsu domin jama’a su kai gaisuwar ban girma ga marigayi Dattijon Jiha da qasar
Bugu da qari, za a buxe rajistar ta'aziyya ga jami'an diflomasiyya da sauran jama'a a ma'aikatar harkokin waje da cibiyar taron qasa da qasa ta Bola Ahmed Tinubu, Abuja.
Qarin taƙaitaccen bayani zai biyo baya yayin da kwanakin zaman makokin ke gudana