ƘUNGIYAR WASAN POLO TA KATSINA TAYI TA'AZIYYAR TSOHON SHUGABAN ƘASA MUHAMMADU BUHARI

ƘUNGIYAR WASAN POLO TA KATSINA TAYI TA'AZIYYAR TSOHON SHUGABAN ƘASA MUHAMMADU BUHARI 
Shugaban ƙungiyar Polo ta Katsina Dokta Muhammadu Usman Sarki a madadin membobim ƙungiyar na miƙa ta'aziyyar rashin Uba, Majiɓanci kuma babban jagora tsohon shugaban ƙasar Najeriya marigayi janar Muhammadu Buhari wanda Allah ya karɓi rayuwar shi a ranar Lahadi a wata asibiti a garin Ingila bayan yayi wata gajeruwar jinya. "Mun yi baƙin ciki tare da miƙa wuya ga yardar Allah (SWT) kan rasuwar majibincinmu, dattijo, uba kuma tsohon shugaban kasa, Muhammad Buhari. 
Ba wai kawai ya kasance babba mai halin kirki a cikin aikinsa na soja da siyasarsa ba, hatta abokan gaba sun yarda cewa Baba Buhari za a tuna da shi har abada a tarihin Najeriya". 
Ƙungiyar ta Polo ta mika ta'aziyyar ta ga iyalansa na kusa, Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Sarakunan Katsina da Daura da ƙasa baki ɗaya kan wannan rashi da ba za a iya gyarawa ko mantawa ba. 

Post a Comment

Previous Post Next Post