ƘUNGIYAR NURTW TA JAHAR KATSINA TA JAJANTAWA GWAMNA RADDA TARE DA ADDU'AR SAMUN LAFIYA

ƘUNGIYAR NURTW TA JAHAR KATSINA  TA JAJANTAWA GWAMNA RADDA TARE DA ADDU'AR SAMUN LAFIYA

Ƙungiyar Direbobi ta ƙasa NURTW reshen Jahar Katsina ƙarƙashin jagorancin Alhaji Musa 'Yandoma ta jajantawa Gwamnan Jahar Katsina Malam Umar Dikko Radda akan hadarin motar da ya rutsa da shi akan hanyar Katsina zuwa Daura tare da wasu dake tare da Gwamnan. Alhaji Musa ' Yandoma wanda ya nuna alhinin ƙungiyar tare da ƙara roƙon Allah da ya kawowa Gwamnan sauki domin ya cigaba da aikin shi kamar yadda ya saba. Kazalika, Shugaba Alhaji Musa ya kara addu'ar samawa marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari gafara tare da samun rahamar Allah. 
Alhaji Musa 'Yandoma wanda ya mika sakon alhini a madadin dukkan membobin ƙungiyar jahar. Ya kara da cewa, wannan rashi na shugaba Buhari rashi ne wanda ya shafi kasa baki daya. Kazalika, hadarin da Maigirma Gwamna ya samu, al' ummar jahar ne baki daya suka samu hadarin. Yayi fatan Allah ya kara tsare gaba ya kuma sa kaffara ce. 



Post a Comment

Previous Post Next Post