ANYI KIRA GA GWAMNATIN JAHAR KATSINA AKAN TA SAKE DUBA MAJUYIN HANYAR KOFAR SORO - KOFAR GUGA

ANYI KIRA GA GWAMNATIN JAHAR KATSINA AKAN TA SAKE DUBA MAJUYIN HANYAR KOFAR SORO - KOFAR GUGA 
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
"Gaskiya Gwamna Malam Dikko Umar Radda ya cancanci a yaba mashi akan irin yadda yake gine-ginen hanyoyi a fadin jahar Katsina domin samun saukin tafiya da mu'amulla a tsakanin jama'a".
Wani matashin ɗan kasuwa Zahradden Lawal ya taya Gwamna Radda murnar zowar Mataimakin Shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima ziyarar aiki ta kwana biyun da yayi ya koma gida lafiya, bayan gudanar da wannan ziyara cikin kwanciyar hankali tare da samun kyakkyawar tarba daga al'ummar jahar. Zahradden wanda ya kwatanta Gwamna Radda da marigayi tsohon shugaban ƙasa Malam Umar Musa 'Yar'aduwa wajen ƙoƙarin ya ciyar da jahar da al'ummar ta gaba ta fuskoki dabam-dabam.
"Hanyoyi na daga cikin abubuwan da suke ciyar da al'umma gaba ta fuskar kasuwanci, noma da kiwo tare da sada zumunci a tsakanin jama'a. Gwamna Radda duk ya gama wannan aikin lada. Idan ka dubi musamman mu masu ƙananan sana'o'i ba ƙaramin ci gaba wannan aiki na hanya. To sai dai muna da koke ko kira ga Gwamna musamman akan waccan babbar hanya wadda take ta tarihi anan cikin garin Katsina, wato, hanyar da ake cewa 'IBB WAY' wadda ta taso tun daga Kano har zuwa kan iyaka da Nijer. Ita babbar hanya ta farko wadda ta ratso cikin garin Katsina tun ma kafin a samu jahar. To amma wannan aikin faɗaɗa titin da aka yi wanda ya faro daga sha-talai-talai na Ƙofar Soro zuwa Ƙofar Guga ya kashe wannan titi mai dimbin tahiri".
Tun daga Ƙofar Soro har zuwa Ƙofar Guga ace majuyin hannu (U-turn) guda ɗaya ne gaskiya ba ƙaramin kashe wannan titi aka yi gami da harkokin kasuwancin da ake yi ga kuma unguwannin dake amfana da shi ta fuskar ƙananan sana'o'in da mata kan yi a bisa shi. Mai girma Gwamna, majuyin bakin CPC da na Gobarau da na kasuwar Chake da kuma titin Usman Sarki da aka kashe gaskiya ba ƙaramin takurawa ba ce ga wannan al'umma. Wannan majuyi guda dake kusa da shagon Ɗanshinkafi mai canji, in baya ga ƙara hadda matsala da kuma haɗari a tsakanin ababen hawa babu abin da ya taimaka da shi. Kowane sashe idan yana so ya juya ɗaya ɓangaren, bayan ya karkato ya shigo, dole sai ya sake komawa baya kafin ya sake shigowa ya fice. A gaban mu mun sha ganin walau na ɗaya hannun da za'a shiga ko inda za'a fito an samu fitowar wani wanda yake bisa titin kai tsaye an samu yin arangama saboda ƙarancin wurin juyawar. Sannan rashin samun wurin juyawar ya kashe wancan gidan tarihi na Gobarau bayan kuma wannan haryar zata fita har bisa hanyar da ta fito daga Ƙofar Sauri zuwa Ƙofar Soro. Sannan ga asibitin ido dake bisa wannan hanya".
Lura da waÉ—annan abubuwa yasa matashin É—an kasuwar yayi kira ga Gwamna Malam Dikko Umar Radda da gwamnatin shi da su dubi wannan lamari na sake bude wurin juyawar ababen hawan dake bisa wannan hanya ta IBB da kuma Ƙofar Soro zuwa Ƙofar Guga. Har ila yau, Zahradden ya Æ™ara jinjinawa Gwamnan bisa karÉ“ar baÆ™uncin taron yiwa kundin tsarin mulkin jama'iyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma da Gwamnan yayi. "Wannan ma ba Æ™arin ci gaba bane a wannan gwamnati", inji Zahradden Lawal. 

Post a Comment

Previous Post Next Post