Hajj2025: Rahoto na musamman - YADDA MUKA GUDANAR DA AIYUKAN HAJJI - Mahajjatan jahar Katsina

Hajj2025: Rahoto na musamman - YADDA MUKA GUDANAR DA AIYUKAN HAJJI - Mahajjatan jahar Katsina 
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Kamar sauran mahajjatan duniya, mahajjatan jahar Katsina na daga cikin waÉ—anda suka gudanar da aiyukan Hajjin bana na 2025 abin da ya fara tun daga ziyarar kabarin fiyayyen halitta Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wassalama da ziyarar sauran wurare a garin Madina har ta kai komawar su a garin Makka don yin Umra da kuma zaman jiran babbar ranar aiwatar da wannan aiki na Hajji wato, ranar Arfa. Mahajjatan sun kuma samu damar sabke wannan farali a ranar alhamis 9 ga Zulhajj 1446 wadda tayi daidai da 5 ga watan Yuni, 2025. Mahajjatan bayan sabke wannan farali sun wuce zuwa MuzÉ—alifa inda suka kwana a bisa hanyar su ta zuwa Jamrat domin yin jifar farko da kuma dawafin farko gami da sa'ayi bayan kammala waccan farilla ta Arfa.
Wakilin mu ya samu damar tuntuɓar wasu daga cikin mahajjatan ta wayar salula don jin ta bakin su akan yadda suka gudanar da wannan aiki. Alhaji Salisu, yace, "duk da wannan ne zuwa na farko a wannan aiki, gaskiya banyi zaton samun natsuwa da samun damar yin wannan aiki ba kamar yadda na riƙa jin ana bayar da labarin irin yadda ake yin aikin. Tun farko, kafin in baro garin mu wanda ba zan gaya maka, na fara samun natsuwa ta irin yadda aka riƙa yi mana bitar yadda ake aikin har zuwa lokacin da na zo Katsina don shiga jirgi. Na gamsu da irin yadda jami'an wannan hukumar jin dadin Alhazai ta rika kula da mu, duk da cewa, wasu lokuttan bamu samun wasu bayanan da yakama mu samu a tsaikon jirgin da aka samu. Amma gaskiya, har zuwa yanzu maganar da nike yi da kai anan garin Makka, in baccin da aka ce aikin dole ne ake samun wasu 'yan matsalolin da kowace shekara ake samu, to da nace, ni kam ban fuskanci kowace irin matsala ba.
Hajiya Badiya Bakori tace, irin yadda mata suka samu kulawa a wannan aiki, gaskiya a shekarun baya can bata yi zaton haka ba. "Na ɗauki shekaru da yin aikin hajji, amma yadda naga a bana yadda aka kula da mu mata abin ya bani sha'awa ba kamar wancan lokaci ba da yawan bacewa kaɗai ya ishe mu. Illa dai kawai su jami'an da aka azawa nauyi musamman na ƙananan hukumomi yana da kyau su ƙara bayar da himma domin aiki ne mai nauyi akan su. Na lura, wasu baƙin aikin ne, amma hakan ba zai hana su tuntubi na saman su ba. Sannan batun faɗakarwa, gaskiya mun samu ilmi sosai daga su masu wa'azin mu sashen mata. Ba sai nace, malama wance ko wancen ba, sun yi iya kokarin su matuƙa.
Alhaji Aminu Ahmad Wali, wanda yake tsohon Alhaji ne, kuma shi ne shugaban ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu na jahar Katsina, kuma shugaban ƙungiyar wasanni ta matasan jahar, jinjina yayi ga hukumomin da abin ya shafa na aikin Hajji na jahar baki ɗaya. Alhaji Aminu ya ce, tun daga gida Najeriya ya fara lura da irin tsare-tsaren da aka yi na wannan shekara waɗanda aka samu shigo da wasu sabbi wanda sai mutun ya lura zai gane haka. "Ni a jirgi na farko na taho, amma ko a batun hudubar kiyaye dokokin Saudiya da aka yiwa mahajjatan gaskiya abin yayi tasiri sosai. Sannan babu wani mahajjacin da naji yayi wani ƙorafi akan ba'a bashi wata takarda ko wani abinda zai kare mutuncin shi ba, misali, katin sheda mai dauke da hoton mutum. Sannan ko a zaman mu na Madina, duk da cewa, duk wata hidima acan ƙarƙashin hukumar kula da aikin Hajji ta ƙasa NAHCON ke yi, hakan bai hana jami'an hukumar jin dadi na jahar su taimakawa mutanen su ba".
Shugaban ƙungiyar dillalan man fetur kuma tsohon Alhajin ya ƙara da cewa, babban abinda ya ƙara burge shi ba kamar yadda shi Amirul Hajjin ya riƙa kai gwabro da mari a tsakanin mahajjatan jahar domin jin ko akwai wani mai ƙorafi ko wata matsala domin ganin an ɗauki mataki. "Wato, sai ince gaskiya, ni dai a wuri na, wannan karon Gwamna Malam Dikko ya sanya jajirtaccen jagora. Mutumin nan shi ne Mataimakin Gwamnan jaha fa, amma kai in kaga yadda yake shiga cikin jama'a abin zai baka mamaki. Babban abin da ya ƙara burgi ni da shi shine, a zaman mu na Minna. Ace Amirul Hajji kuma Mataimakin Gwamna amma da shi ake bi Hema-hema domin ganin halin da ake ciki. Kai ƙarshe ma da shi ake gyaran shimfidun da mahajjata ke kwanciya. Ka dubi girman kujerar Mataimakin Gwamna kuma jagoran mahajjata, amma shi ke gyaran inda mutumin cikin karkara wanda ya saba kwanciya ko'ina, amma Mataimakin Gwamna ke sa hannu ya gyara mashi abin kwanciya. Wannan ba ƙaramin tsari da cigaba ba ne a wannan aikin Hajji na bana. Ni dai kam, tun tsawon lokacin da na dauka ina zuwa wannan aiki ban taɓa ji ko gani ba", inji Alhaji Aminu Wali
A lokacin da wakilin mu ke Æ™oÆ™arin 
kiran wani mahajjacin, sai yayi kiciɓis da wani Bafillace wanda yace, wayar a hannun shi take, mai ita baya nan. Wakilin yayi amfani da wannan dama domin jin ta bakin wannan Bafullatani. "Ni kake son jin sunana? To Alhaji Bammi nike. Gaskiya inda son raina ne to sai ince na zo kenan. Yo daɗin ai yayi yawa. Kullum sai mutun ya ci kaza ya sha lemu? Yo malam ai ko a aljanna abinda mutun yake son ya samu kenan. Wallahi in baccin da barci yana ɓarawo, ai da nace ko barci kada inyi. Mutun ga shi ga ɗakin Allah, to me kuma zai nema? Da aka tuntube shi abinda ya fi burge shi, sai yace, baya ga ziyarar kabarin Annabi da kuma yin zagayen ɗakin Allah, sai kuma ranar da aka ce ya zama cikakken Alhaji, wato, yayi Arfa. "To mai tambaya in gaya maka, banda waɗancan sai kuma ganin Mataimakin Gwamna da nayi, gani ga shi babu wani shamaki. Harma ƙara gusawa nayi kusa da shi da aka ce shine. Habawa, sai kuma ranar da naga Gwamna Dikko Radda. Bayan ance ya biya mana kuɗin yanka, kuma da kunne na naji ya bamu kudin Saudiya har 300. Ciki dai har uwargida na sayowa abin rataye, da kana kusa da na nuna maka shi".
Shi kuwa Alhaji Almu Hamisu kira yayi ga hukumar dake kula da Aikin Hajji ta kasa NAHCON cewa, ta mayarwa jihohi aikin kula da harkokin kiwon lafiya da kuma hemomi a zaman Minna. "Yanzu idan ba don gwamnatin jahar Katsina ta turo da wakilcin ma'aikatan lafiya ba, ina tabbatar maka da batun zafin ranar da ita Saudiya tayi gargadin a kiyaye ba, da shi kadai ya isa wani abin damuwa. Amma ma'aikatan sunyi iya ƙoƙarin su wajen faɗakarwa. Sannan wani abin dabam shi ne, hatta da yadda aka tsara hemomi da kayan shimfidar da aka sanya, amma sai ga shi Maigirma Mataimakin Gwamna shi ke zuwa da kan shi ana yin gyara, inda ace jaha ce ita NAHCON ta sakarwa mara tayi da kanta, ita ta zamo mai sa ido, da duk wadannan abubuwa basu samu ba. Gaskiya na jinjinawa shi Amirul Hajji da sauran su jami'an hukumar jin dadin Alhazan na jaha. Sun yi iya ƙoƙarin su.
Da muka nemi jin ta bakin wasu daga cikin jami'an hukumar jin dadin alhazan ta jahar Katsina, wanda muka samu kuma ya nemi a sakaya sunan shi ya ce, "gaskiya a daɗewa ina aiki a wannan hukuma, ban taɓa gani ko aiki da wani Amirul Hajji kamar irin wannan ba. Kaga duk da kasancewar shi Mataimakin Maigirma Gwamna kuma Amirul Hajji, wallahi mu dai a namu sashen saidai muce muna godiya. Duk wani mai hakki yana bashi hakkin shi, kuma ya tsaya akan ganin kowa ya tsaya bisa aikin shi. Inda yaga gyara, ba tare da wata hayaniya ko nuna matsayi ba, yana nuna gyaran ko ya bayar da shawara. Babu wanda za'a ce anyi mashi katsalanda a aikin shi. Gaskiya muna godiya matuka musamman ga shi Maigirma Gwamna Malam Dikko Umar Radda akan wannan zaɓen Amirul Hajji da sauran jami'an shi.
Mafi yawan mahajjatan da muka tuntuba suna nuna farin ciki da godiyar ga Gwamna musamman akan daukar nauyin yi masu Hadaya da kuma goron salla na Riyal 300 da ya basu wanda hakan ya taimaka masu matuÆ™a. Kazalika, sun yaba hatta da irin abincin da aka riÆ™a basu tamkar suna gida. 

Post a Comment

Previous Post Next Post