A karo na biyu AN SAKE ZABEN MICHAEL SHUGABAN ƘUNGIYAR 'YAN NAJERIYA MAZAUNA SENEGAL
'Yan Najeriya mazauna ƙasar Senegal sun sake zaben Mista Michael Onkwe Ogugua shugaban ƙungiyar su a karo na biyu. Mista Michael wanda ya fara zama shugaban kungiyar a shekarar 2023 ya kawo sauye - sauye a zamantakewar 'yan Najeriyar mazauna ƙasar ta Senegal. Kamar yadda ya shaidawa wakilin mu a hirar da suka yi ta wayar tarho yace, lokacin da yake zaune acikin ƙasar ya lura da cewa 'yan Najeriya na zaune kara zube babu wata haɗaɗɗiyar ƙungiyar wadda zasu riƙa haduwa suna tattaunawa a matsayin su na baƙi.
"Lokacin da na shiga waccan takara ta 2023 nayi nasara, abu na farko da na fara yi shi ne, neman hukumomin jami'an tsaron ƙasar ta Senegal domin baiyana masu damuwar mu akan yadda 'yansandan ƙasar ke yawan kama 'yan Najeriya suna tsarewa ba tare da wani laifi ba. Suna shiga gidajen da mutanen mu ke zaune su kwashe masu kaya ko su ƙulla masu wani laifin da basu aikata ba don su ci zarafin su. To a matakin ƙungiya na jagoranci zuwa har babban ofishin hukumar tsaron ta ƙasa bayan samun haɗin guiwar Ambasadan Najeriya dake ƙasar. Wannan matsalar a yanzu babu ita".
Shugaba Michael ya ci gaba da cewa, bayan nemarwa 'yan Najeriya samun walwala ba tare da tsangwama ba, abu na gaba da suka yi shi ne, "ganin mafi yawan mutanen mu suna zaune babu aikin yi, mun bi kamfanoni da masana'antu domin samar da ayyukan yi wanda kuma aka samu nasarar yin haka. Yanzu dai ina iya shaida maka cewar da wuya a samu mai zaman banza a ƙasar wanda ya fito daga Najeriya. Kazalika, hawa na bisa wannan kujerar shugabanci na kawo bikin nuna al'adun 'yan Najeriya wanda muke yi a duk shekara, kuma abin yana armashi da kuma ƙara danƙon zumunci a tsakanin mu da kuma nunawa sauran duniya cewar muna da al'adun gargajiya masu kyau a Najeriya. Banda wannan, muna yin bikin samun 'yancin kai na Najeriya. Muna haɗuwa muyi biki na murna".
Mista Michael har ila yau, ya ce, zaman shi shugaban 'yan Najeriya mazauna ƙasar ta Senegal yayi ƙoƙarin ganin cewa a duk inda 'yan Najeriya suke da zama a ƙasar sun kafa ƙungiya domin ƙara danƙon zumunci da kuma taimakon juna. "Ina tabbatar maka cewar a yanzu babu inda babu irin wannan ƙungiya ta 'yan Najeriya acikin birane da ƙauyukan da suke zaune. Kuma kullum sai ƙara samun nasara muke yi".
Sai dai Shugaba Michael ya nuna damuwarshi akan irin yadda wasu marassa kishi ke yaudarar wasu 'yan Najeriya musamman mata masu ƙananan shekarun da basu wuce 18 ba da sunan zasu kawo ƙasar don samun aikin yi amma a ƙarshe su faɗa harkar karuwanci ganin cewa ƙasar ta Senegal bata hana yin sana'ar karuwanci ba. Akan haka yake yin kira ga al'ummar Najeriya musamman iyaye da su matasan da ake yaudara da su riƙa sanin mutanen da suke harkar da su tare da yin taka tsantsan ga masu cewa zasu samar masu da aikin yi a ƙasashen waje.
An sake zaben shi Shugaba Michael A. Agugua tare da sauran shugabannin ƙungiyar da suka haɗa da, Owen Kingsley Mataimakin Shugaba, Jimoh saheedu musa Babban Sakatare, Emmanuel Okata Ma'aji. Sauran su ne, Ibah Joseph Killian Sakataren kuɗi da Ibrahim lukuman Mataimakin Sakatare da Mokobia Rhoda Sakataren jin dadi tare da Maidoki Abdullahi Mataimakin Sakataren jin dadi. Sai kuma iyayen ƙungiyar da suka haɗa da Imam Musa Hassan Katsina da Pastor Aphams mosses Abia