Mutuwar Janar Buhari: GWAMNATIN JAHAR KATSINA TA CE RANAR LITININ BA AIKI

Mutuwar Janar Buhari: GWAMNATIN JAHAR KATSINA TA CE RANAR LITININ BA AIKI
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 

A wata sanarwar da Daraktan Labarai na ofishin Sakataren gwamnatin Jahar Katsina Alhaji Abdullahi Aliyu 'Yar'adua ya sanyawa hannu tace, Gwamnan Jahar Malam Dikko Umar Radda ya bayar da hutu na ranar Litinin ga ma'aikatan jahar domin girmama marigayi tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari wanda Allah ya karbi rayuwarsa a ranar Lahadi a wata asibiti dake London. 
Kamar yadda sanarwar ta ce, Sakataren gwamnatin Jahar Barista Abdullahi Garba Faskari ya sanar cewa, gwamnatin Jahar ta dauki wannan matakin yin hutun domin baiwa ma'aikatan jahar damar haduwa da sauran jama'a domin jimamin da alhinin wannan babban rashi. 
Shi dai marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya bar duniya yana shekaru 82. Allah ya karbi ransa a wata asibiti dake garin London bayan yayi jiyya. Kamar yadda Gwamna Radda wanda a yanzu haka yana London ya ce, suna sa ran kawo gawar marigayi a wannan rana ta Litinin domin ayi jana'izar shi a Daura mahaifar shi. 

Post a Comment

Previous Post Next Post